KIWON KAJIN HAUSA A ZAMANANCE 3
Tsarin Da Ake Bi
Duk Kaji guda goma ana sayan zakara guda daya ne wato za a sayi kaza guda goma sai zakara guda daya ya zama na sha daya.
In an kawo su gida sai a lura da su ta yadda za a koya musu cin abinci tare saboda an sayo su daga mabanbantan gurare.
Sai kuma a tabbatar an koya musu yin kwai da kyankyashe shi a lokaci guda.
Ta yaya za a koya musu haka?
To ga shi an tanadi gurin ajiye kaji kuma har an sayo su an zuba a daki.
Ya za a yi?
Za a bar su a cikin dakin har tsawon kwana uku ko Biyar yadda za su saba da dakin in sun fita za su dawo ciki.
A tabbatar an yi musu antibiotics a lokacin da aka kawo su.
In ba a guri daya aka sayo su ba *kar a hada su guri daya kafin a yi musu antibiotics*
A yi amfani da na bature (synthetic) ko kuma na gargajiya.
Ya ya kamata dakin kajin ya zama?
Ku biyo ni a kashi na Hudu…
HausaFarmers Community
Kabiru Muhammad
08089296555
#hausafarmers #manoma #noma