MAFITA GAME DA KWARAROWAR HAMADA A YANKIN AREWA 1

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mako a wannan mudawwana tamu ta noma da kiwo wacce take tattauna al’amuran noma da kiwo musamman a wannan yanki namu na arewacin najeriyya. Wannan makon da yardar mai duka zamu tattauna akan wannan bakuwar matsalar nan da tak ci taki cinyewa wato matsalar kwararowar hamada wanda da muke jin labari daga kasashe masu nisa to yau gata a kofar gidanmu illah iyaka muyi kokari wajen samar da mafita kafin wankin hula ya kai mu dare.

Kwararowar hamada na daya daga cikin manyan matsalolin da mafi yawancin jahohin arewacin wannan kasa suke fama da ita. Jahohin nan sun hada da sokoto,kebbi,zamfara,yobe,jigawa kano,bauchi,katsina inda kuma tafi kamari shine jahar borno(inda ta mamaye ku san gabaki dayan yankin kudu na jahar). Inda ta haifar da koma baya a habbakar noma sakamakon mamayar da  tulin rairayi yayi wa filayen noman. Har ta kai ga ministan muhalli na najeriyya yayi hasashen cewa a dukkan matsalolin da wannan kasa take fuskanta a bangaren muhalli ,kwararowar hamada ce babbar kalubale na muhalli a kasar nan, wanda in ba an tashi tsaye anyi maganin taba zai haifar da mummunan karancin abinci sakamakon afkuwar fari da hamadar kan haddasa. Bincike ya tabbatar da cewa karancin ruwan sama da ake samu a duk shekara, afkuwar fari da lalacewar kasar noma ya samo asali ne da wannan matsala ta HAMADA.

MENENE HAMADA ?

Hamada kamar yadda muka sani shine lalacewar kasar tudu (dryland). wanda tana faruwa ne sakamakon abubuwa da dama kamar canjin yanayi daga Allah da kuma ayyuka ko mu’amalolin dan’adam na yau da kullum. Haka nan hukumar abinci da noma ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa kwararowar hamada ita ce babbar matsalar muhalli a duk fadin duniya inda suka fassara kwararowar hamada da kyakykyawra kasa ta koma sahara sakamakon saran bishiyoyi,fari, ko noman gona ba bisa ka’ida ba.

TAKAITACCEN TARIHI

Hamada a duk fadin duniya ta  samo asali daga yanayi da yake kai kawo a lokaci mai tsawo daya gabata.cikin yawancin wadannan lokuta hamada tana fadada da kawo tasgaro ga ayyukan yau da kullum na dan’adam. Wadansu girman su ya zarce hankali kamar wannan babbar hamada ta duniya wadda ake kira da SAHARA.Kwararowar hamada ta taka rawar gani a zamantakewar dan’adam, inda ta taimaka gaya a wajen faduwar mafi yawa daga manya-manyan daulolin duniya kamar su daular girka, daular rumawa da sauran su.

INDA HAMADA TA SHAFA

Bincike ya nuna wajen kashi 40-41 cikin dari na duniya tudu ne wanda ya zama matsuguni ga mutane kimanin biliyan biyu, sannan an kintaci cewa kashi 10-20 cikin 100 na tudu a halin yanzu hamada ta cinye wanda ya kai gwargwadon murabba’in kilomita miliyan 6-12, ya nuna kenan kashi 6 cikin 100 a halin yanzu suna rayuwa ne a cikin hamada, sannan akwai kimanin mutane biliyan daya da suke cikin dar-dar na mamayar hamada .kamar yadda muka fada a baya cewa SAHARA ita ce babbar hamada a duk fadin duniya a halin yanzu tana matsawa kudu da gudun kilomita 48 a duk shekara.

ME KE KAWO HAMADA.

Sannan abin da yake kawo wannan annobar ta hamada shine mummunar dabi’ar nan ta nutanen mu na yawan sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba, sannan ko da an sare don wata bukatar zaka ga shi ke nan ba za’a sa wata a madadin wannan wadda aka sare ba. Abi na biyu shine yawan noman gona akai-akai ba kakkautawa, domin yawan noman gona yana sa sinadaran dake cikin kasa su kare dai-dai lokacin da ba zata iya samar da wadan suba. Wannan yafi faruwa ga masu noman rani shine nake ganin ya kamata nai kira ga manoman rani da su tabbata suna bin shawarar kwararru don kaucewa irin wadannan matsaloli.

Mai Rubutu: Auwal Abdulqadir Sani

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here