GABATARWA
Idan aka yi maganar kajin gida ba sai an yi dogon bayani ba kowa ya san me ake nufi. Musamman yanzu da ake fama da tsadar abincin kaji. Ga kuma matsalar kasuwa in na turawa ne. Amma Kajin Hausa har gida za a zo a saya da kuma daraja. Gaskiya wannan kiwo yana da matukar riba sosai kuma ba shi da kashe kudi kamar kajin zamani, ga kuma suna da saukin sha’ani da rashin laulayi nan da nan za a iya Tara kaji masu matukar yawa. Misali, za a iya da kaji goma za su iya zama dubu biyu a ciki shekara daya ko kasa da haka.
DAKIN KAJI KO KEJI
Wannan kiwon SEMI INTENSIVE ne saboda za a bar su suna fita kiwo Za a samu daki ko keji Wanda aka tanada don kiwon. Kafin a kawo su za a tanadi mazubin abinci( feeders) da kuma mazubin ruwa(drinkers) sai kuma tittikar katako ko buntu ko duk wani Abu da za a zuba domin kajin suna takawa. Sai kuma a tanadi akurki(nest box) adadin yawan kajin da ake bukata. Dakin ya zama yana da wadataccen wajen shan iska(ventilation).Kuma in daki ne ya zama kofar tana kallo Arewa ko Kudu.
A tabbatar an yi kofar da bera ba zai shiga ba.
Kafin sayo kajin da kwana uku ko biyu a sayo maganin kwari kowanne iri ne a fesa a dakin. Ranar da za a sayo kajin sai a baza wannan tittikar katako ko dai abinda aka tanada. Sai kuma a zuba ruwa da abinci a wannan mazubai sai a rufe dakin a tafi sayen kaji.
Kabiru Muhammad
#farming#hausafarmers#nimet#noma#damuna#manoma#poultryfarm#poultry
Shafin ya yi kyau sosai kuma darasin ya fita
Allah Ya taimaka
Allah Ya saka da alheri
Muna godiya sosai