NOMAN MASARA

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan mudawwana ta noma da kiwo da fatan ana samun waraka daga abubuwan da muke tattaunawa a wannan mudawwana tamu Allah yasa mu dace AMIN.A wannan mako zamu yi bayani ne akan wannan amfanin gonar mai dadadden tarihi, mai gina jiki da kuma juriya daga kwari. Bincike ya tabbatar da ana girbe sama da tan miliyan 800 na wannan amfani gona a fadin duniya. Da yardar maiduka zamu tattauna ne akan Asali, takaitaccen tarihin masara, yadda ake noman masara musamman a wannan yanki namu da kuma alfanun dake tattare da wannan amfani gona mai tsohon zamani.

TAKAITACCEN TARIHI

Masara tana daga dangin ciyayin nan da ake kira da GENIUS POECAE, wanda suka kunshi fiye da kala dubu na na ciyayi. Masara kamar yadda muka sani tana da yanayi da hatsi kamar Alkama, Dawa da sauran su.Hujjojin kimiyyar aikin gona sun tabbatar da cewa yabanyar da a yanzu muka santa da Masara an fara gano tane  wajen shekaur 7000 kafin haihuwar Annabi Isa da suka shude, daga cikin ganyayyakin dajin nan wato TOASINTE. Masarar  yanzu ta sha ban-ban data waccan zamani domin kuwa kusan har yawancin manoman mu na yanzu bana tsammanin sun san cewa waccan masara ta dauri tafi ta wannan zamani kankanta da dandano ba kamar irin ta yanzu ba. Haka abin yaci gaba da tafiya har zuwa shekara ta 1500 kafin haihuwar Annabi Isa, inda turawan daji (mesoamerican) suka zamanantar da masara tahanyar amfani da dabarun noma zuwa yadda muke ganin ta a yau. A karni na 16 zuwa na 18 ne, noman Masara ya bunkasa ya shiga dukkan sasannin duniya sakamakon mulkin mallakar turawa, wannan yasa sukekai  irin Masara nahiyoyi da dama kuma ya samu damar karbuwa ga kusan dukkan mutane.

AMFANIN MASARA

Kadan daga cikin amfani da ake da masara shine ana sarrafata a mai da ita gari don yin Tuwo, Kunu da sauransu, idan an tankade ta tsakin ana baiwa dabbobi a matsayin abinci. Hakanan masana’antun maganin zazzabi ma suna amfani da masara domin hade-haden magungunan su da kuma kamfanonin lemuna da makamantansu.Ba haka nan kadai ba kamfanonuwan tufafi ma suna amfani da masara wani zubin a madadin roba.

ADADIN NOMAN MASARA

Bincike ya tabbatar da Masara ita ce amfanin gonar  da aka fi nomawa  a duniya, adadin da ake noma wa kamar yadda hukumar noma da abinci ta majalisar dinkin duniya ta wallafa a shekarar 2005 ya nuna ana noman masara da yakai tan miliyan 692 a duniya.Kasar Amurka inda aka fi noman masara suna noma kashi 40 cikin 100 sauran kakashen da suke mara mata baya sun hada da Cana,Meziko,Indunusiya,Indiya,Faransa, da kuma Ajentina. Binciken baya-bayannan ya nuna ana noma tan miliyan 817 na Masara a duniya inda ake noma kadada miliyan 159.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here