KIWON KAJIN HAUSA A ZAMANANCE 2
Bayan an tanadi gurin ajiye kaji an tanadi mazubin abinci da kuma wajen zuba ruwa
Sai kuma a samo antibiotics mai inganci a ajiye.
ZABEN KAJI
A tabbatar an zabi Kaji masu lafiya da ba su da wata alamun cuta.
YADDA AKE GANE KAJI MASU KYAU DA LAFIYA
1. Kar a sayo wadanda aka ga fiffikensu na yawan sauka ko yawan bude shi suna kasa da shi.
2. Kar a sayo wadanda aka ga alamun ruwa a hancinsu kamar majina ko a idanunsu kamar hawaye
3. Kar a sayi wacce aka ga idanunta da alamun ja
4. Kar a sayi wacce aka ga korarta ta kwanta gefe ko a ga ta yi yaushi ta yi fari-fari.
5. Kar a sayi wadda aka ga jini ko alamun jini-jini a cikin cerar. Wadannan duk alamomi ne na Newcastle Disease, fowl fox da ciccidiosis.
6. Kar a sayi gajurun kaji a samu masu doguwar kafa da kaurin jiki irin na Fulani
7. Kar a sayi wacce kafarta da kurzu-kurzu
Kabiru Muhammad
08089296555
#manoma #kaji #noma #hausafarmera