NOMAN MASARA
Barkan mu da sake saduwa a wannan mako inda muke bayani akan amfanin gona mafi samun daukaka a tsakanin yan’uwansa wato masara, in baku manta ba wancan mako mun yi gabatarwa da takaitaccen bayani da asalin masara da yardar mai duka wannan mako zamu tsunduma yin bayani akan yadda ake noman masara domin kara fadada ilimi da kuma sabbin dabarun shuka na zamani.
Abin na farko wanda na san duk manomin masara ya san wannan shine dole kowace gona da za ai noman masara a cikinta ya kasance a tudu take wato ma’ana bata rike ruwa ko kuma da anyi ruwa nan da nan zata shanye shi a dan lokaci kalilan, sannan ya kasance gonar ta zama tana dauke da albarka wato (nutrient) wanda zasu bawa irin masara taimako wajen saurin fitowa. Kenan mun fahimci cewa noman masara ba a kowace gona ya kamata ayi ba dole sai an bincika an samu wadda ta cika wadannan siffofi da muka ambata a sama.Masana sun raba masarar mu zuwa gida biyu kamar haka;
MASARAR ZAMANI: wato wadda muke ganin ta da farin jiki ko yalo iri masarar zamani yana da yalwa sosai domin manomi ya kan girbi masara da takai Tan 3 zuwa 7 a duk kadada daya bayan haka kuma yana da surin fitowa. Domin kuwa daga fitowarsa ba zai kwana 100 ba zai kosa ga kuma juriya daga kwari da cututtuka kuma koda a kwari ne akan ioya shuka ta kuma ta fito.
MASARAR GARGAJIYYA: Masarar mu ta dauri tana da iri kala-kala kuma a kan hadata da sauranv amfanin gona kamar wake,gyada da sauransu, sannan tana ba da amfani mai yawa in aka girbe.
lokutan shuka masara a wannan yanki namu kamar yadda muka sani shine wannan yanki namu kamar yadda mu kai bayani a baya cewa damunar mu bata da tsayi shine nake ganin zan bawa manoman mu na masara shawarar cewa daga watan hudu zuwa na biyar su tabbatar sun shuka masarar su domin masarar ta kosa da wuri kamar yadda muka fada a baya. Sannan a kiyayi yin noman masara akasan inda itatuwa suka lullube don a kaucewa lullumi wanda yake zama illa ga girma da kosawar masara.
Masarar mu ta gargajiyya mai kalar ja da fara za’a shuka irin ta mai nauyin kilo 18 a cikin kowace kadada daya. Akan sa daya ko biyu cikin kowane rami. Sannan yana da kyau a bar ratar kamu uku a tsakanin kowace shuka. Yayin da masarar zamani kamar yadda masana suke bayar da shawara cewar ya kamata a dinga barin ratar santimita (centimeter) 90 yayin da tsakanin kunya zuwa kunya a dinga barin santimita 34.Ana bukatar iri mai nauyin Tan 25 a kowace kadada daya inda za’a dinga sa iri biyu a duk rami daya.
Abi na gaba shine taki wanda mukai mukalar sa a baya, to masara akan watsa mata takin zamani ko na gargajiyya. Manomin masara kan iya watsa taki a gonarsa kafin yayi shuka ko kuma bayan yayi shuka, a lura cewa ba kowane taki na zamani ko na gargajiyya ba za’a watsa a gonar masara ba wato ya kasance an tantance wane taki ne zaifi dacewa ga masara.
Masara na bukatar nome ciyayin da suke kusa da ita kafin ta girma, sannan anai mata feshin maganin kwari

Mai Rubutu: Auwal Abdulqadir Sani
Gaskiya Allah ya saka da alheri
Ameen ya Allah