KASAR NOMA DA KIWO A NAJERIYYA
TSARIN MALLAKAR KASA A NAJERIYYA
Tsarin mallakar kasa shine hanya da ake bi domin wannan kasar ta zama taka wato hakkin mallaka da ikon yin kowane tasarrufi da ita a kuma kowane lokaci ga mtum,ko yan gari,ko gwamnati ta hanyar amfanin wucin gadi kona din din din.Amma zahirin magana shine wannan tsarin ya sha bam ban ga wasu kabilu,ko mutan gari ko kuma gwamnati.Da haka ne zamu iya cewa ana mallakar kasa ne ta wadannan hanyoyi kamar haka:

- Hakkin mallakar kasa ga yan gari: wannan tsari yana bawa duk dan gari damar yin amfani da kasar garin domin hakkin mallakar na yan garin ne baki daya,kenan duk dan garin yana da iko amfani da kaasar garin wajen yin noma ko kiwa ko gina gidan da zai zauna da dai sauran su.Sai dai bashi da ikon sayar da kowane bangare na wannan kasa.
- Tsarin mallakar kasa ta hanyar gado:wannan tsari yana bada damar mallakar kasa ta hanyar gado wato daga iyaye zuwa ga yayensu. Kazalika wannan tsarin shi aka fi amfani da shi a wannan kasa saboda duk yawancin gonakin noman kasar nan na birni da karkara za ka ga masu su sun mallake sune ta hanyar gado.
-
Tsarin bada hayar gona:wannan tsri ya ba da damar bada aro ko hayar gona yayin da wanda aka bawa a hayar nan zai dinga biyan wanda ya bashi hayar nan kudi ko wani yanki na amfani gona a tsawan lokacin daya zauna ya amfana da gonar.
-Tsarin siyan kasa:shi wannan tsarin yana bawa mutum damar sayan kasa don amfanin kansa. -
Tsarin yin kyautar kasa da dai sauransu
KASAR NOMA DA KIWO A NAJERIYYA
Kididdigar alkaluma sun nuna najeriyya na da adadin fadin kasa da yakai kadada (hectares) miliyan 92.2 a cikin wannan adadi bincike ya tabbatar da cewar wajen kadada miliyan 91 za’a iya noma akai kuma a girbi amfanin gona mai yawa. Amma bincike ya nuna adadin gonakinb noma a najeriyya yakai fadin murabba’in kilomita 745,000 a binciken baya-bayannan (2009). Tun wajen shekaru 48 da suka gabata wannan adadi yafi yawa a shekarar 2007 inda ya tasamma murabba’in kilomiuta 780,000 yayin da bincike ya nuna gonakin noma sun yi kasa sosai a shekarar 1991 inda alkaluma suka nuna murabba’in kilomita 680,000. Haka nan mafi yawan gonakin noma na wannan kasa ana amfani dasu ne wajen noman kayan abinci da sauransu, yayin da kuma inda ba’a nomawa suka zama dazuzzuka, wato wajen kiwon dabbobi da sauransu. Wani bangaren kuma ba’a amfani da shi ta kowane fannin bunkasar tattalin arzikin wannan kasa. Jahar da tafi kowace kasa a najeriyya yawan yawan kasa da ba’a amfani da ita itace jahar Neja (da kadada miliyan 7.6) sai me biye mata wato jahar Borno (kadada miliyan 2.8)
AMFANIN GONAKIN NAJERIYYA
Alkaluman baya-bayannan sun nuna ana amfani da abin da yakai kadada mioliyan 33 wajen noman amfanin gona a najeriyya. A wannan adadi ana amfani da wajen kadada miliyan 17.7 wajen noman kayan abinci yayin da kadada miliyan 4.9 ake noman kayayayakin masana’antu kamar su auduga da sauransu.
Nan ga kadan daga cikin amfanin gonakin da ake nomawa a najeriyya kuma nan gaba da yardar mai duka zamu dau kowane amfanin gona mu gabatar dashi, yadda ake noma shi, ire-iren sa, yadda ake samai da wane irin taki yafi so,yadda ake ajiyar sa da kuma uwa-uba kasuwar sa. Nan ga kadan daga cikin amfanin gonar da aka fi nomawa a najeriyya.
-HATSI ;dawa,gero,masara,shinkafa da sauransu
-YAN TUSHE ;rogo,doya,makani dankali da sauransu
-LEGUMES ;wake,waken suya,gyada da sauransu.
-KAYAN ZAKI (FRUIT) ;abarba,ayaba,goba,kankana,gwanda da sauransu
-KAYAN MASARUFI\GWARI (VEGETABLES);tumatur,attaruhu,karas,salak,kabeji,tattasai da sauransu
-Mai Rubutu: Auwal Abdulkadir Sani