Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a sassa da dama na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun shaida wa BBC irin ɗumbin dukiya da rayukan da aka rasa tun daga makon da ya gabata.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Bauchi, Sema, ta tabbatar wa BBC mutuwar mutum bakwai a ibtila’in, waɗanda suka rasu sakamakon ruwa mai ƙarfi da kuma ambaliya a ƙaramar hukumar Shira.
Sema ta ce ambaliyar ta shafi sama da gunduma 20 a ƙananan hukumomi kusan huɗu, inda lamarin ya fi ƙamari a yankunan Shira, da Giade, da Katagum, da Azare da ke arewacin jihar.
Mazauna garin Yakasai a Shira sun shaida wa BBC cewa ba su taɓa ganin ambaliya kamar wannan ba a rayuwarsu, wadda ta share amfanin gonaki da dama.
Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ranar Juma’a sun nuna yadda ambaliyar ta yanke tare da haƙa rami a kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri daidai ƙauyukan Malori da Guskuri a ƙaramar hukumar Katagum ta Bauchin.
“Cikin waɗanda suka rasu akwai magidanta uku, da wata tsohuwa da ta kai kusan shekara 80, da ƙananan yara. Akwai waɗanda suka ji raunika kamar mutum takwas,” kamar yadda Abdu Saleh, jami’in hukumar Sema a jihar Bauchi, ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa yanzu haka hukumar na rarraba kayan agaji ga mutanen da lamarin ya shafa waɗanda gwamnatin jihar ta tanada, inda tawagarsa ke aiki a yankin na Shira.
“Dare ɗaya muka tsinci kanmu a irin wannan hali, mu a nan Yakasai ba mu taɓa ganin irinsa ba,” a cewar wani mazaunin yankin mai suna Haruna Shehu.
Abdu Saleh ya ƙara da cewa “tun shekaran jiya [Litinin] muka zo nan, muka zagaya wuraren da abin ya faru, sannan muka rarraba kanmu domin aikin ba da kayan tallafin”.
Shi ma shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Shira, Babangida Ishaq, ya tabbatar da mutuwar mutanen, yana mai cewa sun tsugunar da waɗanda suka rasa muhallansu a makarantu.
“Wasu sun koma gidajen ‘yan’uwansu a ƙauyukan da ke kusa, wasu kuma mun samu kai su makarantu,” in ji shi.
‘Mun yi asarar gona sama da 10’
Wasu manoma a yankin na Shira sun shaida wa BBC yadda ruwan ya share gonakinsu ɗauke da amfani iri-iri.
Haruna Shehu Yakasai na cikin manoman da ke aiki tare da mai garin Yakasai, kuma ya ce ruwan ya shafe musu duka gonakin da suke nomawa fiye da 10.
“Yanzu zancen da nake faɗa maka duka gonakin nan suna cikin ruwa,” in ji shi. “Gonaki na dawa, da shinkafa, da riɗi, babu yadda za a yi mu amfane su.”
“Muna noma gona sama da 10 amma ko rarrabin rabi ba za mu samu ba [na amfanin],” a cewarsa.
Shi ma Mu’azu Yakasai ya ce yanzu ƙoƙarinsu shi ne tsira da rayuwarsu bayan ya yi asarar sama da rabin gonakinsa takwas.
Ya ce: “Ina da gona takwas. Ina da gonar dawa, da shinkafa, da riɗi, da zoɓo, rabinsu duka suna cikin ruwa.”
Wata mai suna Sahura Liman da ambaliyar ta rusa wa gida ta ce babu abin da za su iya yi sai rungumar ƙaddara kawai.
“Ɗakunanmu sun zube, kuma a kwanan nan aka gyara mani ɗakin da nake. Amma da yake ginin bulo ne an sake gyara shi,” kamar yadda ta shaida wa BBC.
Source: BBC Hausa