A wani yunƙuri na shawo kan rikicin shekara da shekaru tsakaninn manoma da makiyaya a Najeriya, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yanke shawarar kafa ma’aikatar kula da haɓaka kiwon dabbobi ta ƙasa.
A ranar Talata ne shugaban ya amince da kafa hukumar, a lokacin da ya kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai kawo sauye-sauyen kiwon dabbobi a fadarsa.
Tinubu ya ce yana fatan ɓullo da sabuwar ma’aikatar zai kawo ƙarshen rikice-rikicen da aka kwashe shekaru ana samu tsakanin manoma da makiyaya.
”Mutane na cewa za a jima ba kawo ƙarshen matsalar ba, amma ni na ce za a magance ta nan ba da jimawa ba, da dama daga cikinku sun san yadda za a magance matsalar domin ciyar da ƙasarmu gaba,” in ji shugaba Tinubu a jawabin da ya yi lokacin kafa kwamitin.
Ya ƙara da cewa idan Najeriya na son cin gajiyar kiwon dabbobin da take yi, dole ne ƙasar ta yi yunƙurin magance matsalolin da ɓangaren ke fuskanta na tsawon shekaru.
Shugaban ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta amince da samar wa makiyayan filayen kiwo domin tabbatar da samun zaman lafiya mai ɗorewa tsakaninsu da manoma.
Yayin da Shugaba Tinubun zai jagoranci kwamitin sauye-sauyen kiwon dabbobin, tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Attahiru Jega zai kasance mataimakain shugaban kwamitin.
Ana sa ran kwamitin zai samar da wasu dabaru da za su inganta zaman lafiya tsakanin manoma da makiyya, domin inganta tsaro da tattalin arzikin ƙasar.
Matakin Tinubun na zuwa ne wata 10 bayan ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasa don magance rikice-rikicen manoma da makiyaya, tare da inganta kiwon dabbobi da samar da madara.
Me zai bambanta sabuwar ma’aikatar da ta aikin Gona
Kiwon dabbobi dai wani sashe ne da ke ƙarƙashin hukumar kula da aikin gona, don haka mutane ke ta aza ayar tambaya kan abin da zai bambanta ma’aikatun biyu.
Mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labarai, Abdulazeez Abdulazeez ya ce kasancewa harkar kiwon dabbobi wani babban sashe ne a ma’aikatar aikin gona ake ganin zai fi kyau a fitar da shi domin mayar da shi ma’aikata mai zaman kanta.
”Kiwon dabbobi kama daga ƙanana zuwa manya, wani babban al’amari ne wanda wasu ƙasashe da dama na duniya suka dogara da shi wajen samun kuɗaɗen shiga da inganta tattalin arziki” in ji hadimin shugaban ƙasar.
Ya ƙara da cewa gwamnati na shirin kafa sabuwar ma’aikatar ne domin faɗaɗa sashen.
”Domin idan ana maganar kiwo ya ƙunshi abubuwa masu yawa, ba wai kiwon shanu kaɗai ba, akwai kaji da sauran dabbobi, sannan akwai ma harkar abincinsu, inda a lokuta da dama akan samu rashin mayar da hankali, ko saɓanin fahimta”.
Ya ce manufar shugaban ƙasa shi ne ɓunƙasa harkar kiwon dabbobi a ƙasar, da magance rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
A farkon wannan shekarar ne dai Shugaba Tinubu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye da ya buƙaci a haɗe wasu ma’aikatun domin rage kuɗin da gwamnati ke kashewa, abinda ya sa wasu ke kallon wannan mataki tamkar mayar da hannun agogo baya ne.
To sai dai Abdulazeez Abdulazeez ya kare matakin da cewa rahoton Oransaye na magana ne kan ma’aikatu da hukumomin da ke cin karo da juna ta fuskar aiki, ko waɗanda aikinsu ba shi da yawa.
”Amma ɓangaren harkar kiwo ai babban al’amari ne wanda ya ƙunshi kiwon dabbobi masu yawa irinsu shanu da raƙuma da kaji, da sauransu, sannan kuma akwai harkar abincinsu da kula da lafiyarsu”.
Ya ce duka waɗannan abubuwa ne masu faɗi da suka cancanci a yi ma’aikata ta musamman domin su.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwmanatin Saudiyya ta bayyana buƙatar sayen nama ton 200,000 da kuma ton miliyan ɗaya na waken soya daga Najeriya, yayin da ƙasar ke son ƙarfafa cinikiyayya domin samun daloli.
Ministan noman ƙasar, Abubakar Kyari ya ce Saudiyya ta amince da buƙatar ne bayan ziyarar da ministanta na noma na ƙasarta ya kawo a Najeriya.
Najeriya ta daɗe tana neman rage dogaro da arzikin fetur zuwa wasu fannoni da za su taimaka wa tattalin arzikin ƙasar.
Me makiyaya ke cewa?
Masu ruwa da tsaki a harkar kiwo sun yi maraba da shawarar da Shugaba Tinubun na ƙirƙiro da ma’aikatar kula da harkokin kiwon.
Alhaji Muhammadu Dodo Orji tsohon shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ne reshen birnin Abuja ya shaida wa BBC cewa sun yi maraba da matakin.
Yana mai cewa wannan abu ne da ya kamata a ce an jima da yinsa, saboda a cewarsa noma da kiwo abubuwa ne biyu da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna.
”Noma da kiwo abubuwa ne biyu da ke tafiya tare, inda akwai noma babu kiwo to akwai matsala, in kuwa akwai kiwo babu noma, to nan ma akwai matsala”, in ji shi.
Ya ce makiyayn ƙasar na maraba da wannan mataki, saboda a cewarsa hakan zai inganta harkokin kiwon dabbobi a ƙasar.
Sai dai ya bayar da shawarar tamƙa sabuwar ma’aikatar a hannun jajirtattun mutane da za su ciyar da ita gaba.
”Muna fatan samun jagororin da suka san abin da suke yi, domin idan aka bai wa waɗanda ba su san harkar kiwo ba, to ba za a samu abin da ake buƙata ba”.
Ya ƙara da cewa manomi da makiyaya abu guda ne, babu abin ya raba su, a tarihin baya akwai yadda waɗannan mutanen biyu ke suhunta kansu idan an samu saɓani tsakaninsu, amma daga baya ƙabilanci ya shiga ya ɓata abubuwa.”
Me manoma ke cewa?
Su ma nasu ɓangare, manoman ƙasar sun yaba da matakin kafa sabuwar ma’aikatar kula dakiwon dabbobin.
Hon. Muhammad Magaji, sakataren yaɗa labaran ƙungiyar manoma ta ƙasar AFAAN, ya ce manoman Najeriya sun jima suna fatan samun wannan ma’aitaka.
‘Domin idan ka je ƙasashen waje da dama da ba su ma kai Najeriya ba, suna da ma’aikatar kiwon dabbobi balle Najeriya”, in ji shi.
Ya ce ƙungiyar Manoma ta yaba da wannan mataki, yana mai cewa suna fatan hakan zai kawo zaman lafiya tsakanin manoma da makiya a ƙasar.
Ya ce makiyaya sun jima suna ƙorafin cewa manoma na cinye musu wuraren kiwo da hanyoyin da suke bi ko an noma wuraren da suke shayar da dabbobinsu, lamarin da a cewarsa ke yawan haifar da rigima.
”To amma idan aka kafa hukumar za ta riƙa shiga tsakanin wajen tsaya wa makiyayan kan haƙƙinsu ba tare da samun fitina ba”, in
Abin da masana ke cewa
Masana tattalin arzikin ƙasa sun ce matakin abin yabawa ne domin zai bunƙasa ƙasar matsawar ya samu kulawar da ta dace.
Malam Yusha’u Aliyu mai sharhi kan tattalin arziki a ƙasar ya ce Najeriya ƙasa ce mai arzikin kiwo tun kafin ta zama ƙasa, ”haka kuma bayan ta zama ƙasa ta yi tanade-tanade domin bunƙasa harkar”.
”Alal misali a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari, ya ɓullo da tsare-tsaren da za su inganta harkokin kiwo, kamar ɓullo da shirin samar da wuraren kiwo ga makiyayan, to amma rashin tsari mai kyau ya kawo cikas ga matakin”, in ji shi.
”Ya ƙara da cewa dole sai an yi tsari mai kyau, a gano matsalolin da ke kawo wa ɓangaren cikas, sannan a kauce musu a wannan sabon tsarin da ake son ɓullo da su”.
Masanin tattalin arzikin ya ce sabuwar ma’aikatar kiwon za ta taimaka sosai wajen inganta tattalin arzikin ƙasar matsawar aka yi tsari mai kyau.
”Alal misali saniya kaɗai idan ka ɗauke ta baya ga amfanin da take da shi a gona da amfaninta wajen samar da taki da samar da madara da amfaninta wajen ciyar da ɗan’adam, akwai kuma abubuwan da za ta samar wa kamfanonin sarrafa abubuwa kamar ƙasusuwanta da fatunta ta kashinta wannan kaɗai zai tallafa wa tattalin arzinkin ƙasar”, in ji shi.
”Yanzu ko fatar saniya da ake amfani da ita wajen yin takalma, idan ka ɗauka a ce ‘yan Najeriya fiye da miliyan 200 za su jira kamfani ya yi musu takalman da za su saka, to ka ga ai lallai wannan ba ƙaramin baunƙasa tattalin arzikin ƙasar zai yi ba”, in ji masanin tattalin arzikin.
Ya ƙara da cewa akwai abubuwan amfani masu yawa kamar abubuwan kwalliya da da ake samu ta hanyar amfani da fatar dabbobi..
Source BBC Hausa