Yayin da damuna ta fara kan kama a Najeriya, gwamnatin jihar Gombe ta fara ɗaukar matakan samar wa da manoma a jihar takin zamani a farashi mai sauki.

Gwamnatin dai ta siyo kowanne buhun takin kan naira dubu arba’in da biyar yayin da ita kuma ta ke siyarwa manoman jihar kan naira dubu ashirin da biyu.

Barista AbdulLahi Jalo, wanda shi ne shugaban kwamitin rabon takin ya shaida wa BBC Hausa cewa ana ci gaba da siyar da takin domin ganin an tunkari gargadin da masana ke yi na barazanar fuskantar karancin abinci a Najeriya.

Ya ce “Shugabannin kannan hukumomin jihar da sai wakilan masarauta, da na mata da matasa da jam’an tsaro” ne ke jagorantar sayar da takin”

Barista Jalo ya musanta wasu rahotanni da ke cewa takin da suke rabawa wanda gwamnatin ƙasar ta ba wa jihohi ne domin su ba wa manomansu a kyauta.

A cewarsa gwamnatin jihar ce ta sayo shi musamman domin saukaka wa manoman jihar da kuma bunkasar ayyukan noma.

“Wanda ake zargi takin gwamantin tarayya ne na NGKS ne, ba a fara raba shi ba ma tukunna, duk da cewa ya zo Gombe, amma kafin nan ma ai gwamantin Gombe ta saba siyo taki ta rabawa manoman kayauta, ba tun yanzu ba” inji shi.

Ya nanata cewa “Kowacce ƙaramar hukuma da ke Najeriya akwai shugabancin ƙungiyar manoma, sannan akwai mai unguwa da dagaci, dukkansu sun san manoman gaskiya da na bogi, shi yasa muka yi imanin cewa manoman ne za su ci gajiyar tallafin gwamantin Najeriyar”

Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan amfanin yau da kullum musamman na abinci, duk kuwa da noman da ake yi a kasar.

A ɓangare guda kuma matsalar tsaro da ake fama da ita musamman a wasu jihohin arewacin ƙasar na tilasta wa manoma haƙura da zuwa gona, saboda tsoron kar ‘yan bindigar su cutar da su.

source: BBC HAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here