Bayan janyewa ko kuma goge sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar game da cire haraji kan wasu kayayyakin abinci da ake shigar da su ƙasar daga waje, yanzu ta tabbatar da aiwatar da yin hakan.
Ministan Noma Abubakar Kyari ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a shafukansa na sada zumunta ranar Laraba, yana mai cewa an cire kuɗin fito, da sauran haraje-haraje a kan wasu kayan abinci.
Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne da zimmar shawo kan matsalar tsadar abinci a faɗin ƙasar.
A ranar Litinin ne mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya wallafa sanarwar, amma sai ya goge ta bayan ‘yan sa’o’i.
Kafin haka, gwamnatin ta sanar da soke harajin cinikayya ga masu ƙananan sana’o’i, ciki har da rage haraji kan sana’o’in da ba su samun riba mai yawa, da kuma soke harajin baki ɗaya ga wasu masu masana’antu da manoma.
Bari mu duba abin da wannan sanarwar ta baya-bayan nan ta ƙunsa da kuma tasirin matakan ga ‘yankasuwa da sauran ‘yan ƙasa.
Waɗanne kayan abinci ne ba za a biya wa haraji ba?
Daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka akwai ɗauke biyan haraji na tsawon kwana 150 daga kan ‘yankasuwar da ke yin safarar kayan abinci daga ƙasashen ƙetare.
Kayan abincin sun haɗa da shinkafa shanshera ko samfarera (wadda ba a gyara ba), da masara, da alkama, da kuma wake.
Kamar yadda ministan ya bayyana, ba za a karɓi harajin ba kan duka kayan da aka shiga da su ƙasar ta iyakokin ƙasa, da kuma na ruwa.
Yaushe za a fara cin gajiyar shirin?
Sanarwar da ministan ya fitar ba ta bayyana takamaimiyar ranar da za a fara aiwatar da shirin ba, amma ya bayyana lokacin da za su daddale hakan.
“Nan da kwana 14 masu zuwa, za mu taru domin daddale tsarin aiwatar da shirin tare da haɗin gwiwar kwamatin shugaban ƙasa kan harkokin abinci, da majalisar tattalin arziki ta shugaban ƙasa, da kuma sauran hukumomin da abin da ya shafa,” a cewar Abubakar Kyari.
Za a aiwatar da shirin da sauran matakai cikin kwana 180 jimilla, a cewar gwamnatin.
Za a ƙayyade farashin kayan abinci ne?
Bugu da ƙari, gwamnati ta ce tana sane da irin damuwar da ake da ita a kan nagartar abincin da za a iya shigowa da su daga waje ƙasashen waje.
Amma dai duk da haka za su ƙayyade wani yanki na farashi.
A cewarsa: “Duka kayan da aka shigo da su za a saka su a tsarin ƙayyade wani yanki na farashi [Recommended Retail Price (RRP)].
“Muna sane da damuwar da ake nunawa game da kayayyakin da ake shigowa da su, musamman game da hanyoyin da ake bi wajen girbe su. Gwamnati na tabbatar da cewa za a bi duk hanyoyin da suka dace na tabbatar da tsafta da lafiyar kayan abincin.”
Wane harajin aka ɗauke wa ‘yankasuwar?
A bayanin Minista Abba Kyari, gwamnati ta ɗauke wa masu safarar haraje-haraje da ta kira duty, da tax, da tariff a Turance.
Duty na nufin harajin da ake karɓa yayin da mutum ya shigo da wasu kaya daga ƙasar waje.
Tax yana nufin duk wani nau’in haraji da gwamnati ke karɓa a kowane mataki; tarayya, jiha, ƙaramar hukuma.
Tariff kuma ka iya nufin harajin da ake cazar mutum kan wasu keɓantattun kaya da yake kasuwanci a kansu.
‘Za mu shigo da ƙarin masara da alkama’
Da yake cigaba da bayani kan matakan da suka ɗauka domin sauƙaƙa farashin abincin, gwamnatin tarayya za ta shigo da masara tan 250,000, da alkama tan 250,000.
“Waɗannan kaya ne da aka fara gyarawa, inda za a rarraba wa ƙananan masu masana’antun gyara hatsi su ƙarasa aikinsu a faɗin ƙasa,” in ji ministan.
“Gwamnati za ta yi aiki da masu ruwa da tsaki domin tsara shirin GMP [Good Manufacturing Practices] kuma ta sayi ƙarin kayan abinci domin cika rumbunan gwamnatin tarayya.”
Ya kuma ce za su ci gaba da yin aiki tuƙuru wajen tabbatar da cewa wasu hukumomi, kamar rundunar soji, sun ƙara ƙaimi wajen noma filayen da suke da su.
“Za mu hanzarta aikin da muke yi da Rundunar Sojin Najeriya wajen noma gonaki a ƙarƙashin shirin Defence Farms Scheme, da kuma ƙarfafa wa sauran hukumomi na ɗamara gwiwar yin amfani da damar da zimmar noma gonaki.”
Wane tasiri matakin zai yi kan manoma a Najeriya?
Manoma a cikin gida na ganin wannan mataki zai shafi ayyukansu, da farashin kayansu, har ma da noman shekara ta gaba.
Muhammad Magaji, shi ne sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar manoma a Najeriya ta All Farmers Association of Nigeria (AFAN), kuma ya faɗa wa BBC cewa akwai hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi ba waɗannan ba.
“Yanzu manoma sun yi noman rani da tsada, shi ya sa abinci ke yin tsada,” in ji shi.
“Sannan yanzu ana cikin damina kuma za a yi noma mai tsada, duk abin da za a noma sai an kashe ƙwarai da gaske. Yanzu kuma sai ga shi an ce an ba da dama a shigo da abinci.
“Saboda haka, idan har abincin da za a shigo da shi ya yi ƙasa da farashin da manoma suka noma kayansu, to lallai zai shafi harkar noma ƙwarai da gaske.”
Sai dai kakakin ya ce da a ce gwamnati ta yi haƙuri kayan za su sauko da kan su saboda tuni aka fara samun amfanin noman ranin da aka yi.
“Ai da ma rashin yin noman rani da aka saba yi ne ya jawo tsadar kayan, waɗanda suka yi kuma sun yi shi ne da tsada sosai. Yanzu kayan sun fara yin sauƙi saboda amfanin da aka noma ya fara shigowa kasuwa.”
Source: BBC Hausa