Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’Adama mai suna Progressive Mind for Developement Initiative, ta bankado yadda wasu masu hannu da shuni sukan tura wakilansu zuwa gonaki, suna saye kayan amfanin gona, tun kafin a kai ga yin girbi.
Haka kuma ƙungiyar ta yi zargin cewar bayan sun saye kayan amfanin sai su boye su, har sai farashinsu ya yi tsada matuka, sannan su futo da shi su sayar.
Ƙungiyar ta ce ta gudanar da binciken nata ne a jihohi biyar na Najeriya, da suka haɗa da jihohin Adamawa, da Benuwai, da Kaduna, da Kano, sai Taraba.
Kwamret Abubakar AbdusSalam, shi ne shugaban ƙungiyar, ya ya ce “ ganin cewar irin wahalhalun da alumma ke fama da su na yunwa da ƙarancin abinci, da ƙarancin kudi da stadar rayuwa, a ƙoƙarin mu na tabbatar da ina aka sami wanna mastala, muka gano cewar akwai masu hannu da shuni da ke shiga har cikin ƙauyuka, su sami manomi har gonarsa, su ɗauki rabin kuɗin aikin gonar su ba su.
Girman Matsalar
Wani wakilin masu tura kuɗi ana yi masu cinikin na falle a jihar Kano, da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce akan tantance girman gona da yaɓanyar da ke cikinta ne sannan a biya manomi.
“Ana bayar da rabin kuɗi, idan mai gona ne zai bayar da ragowa, sai ya yi idan kuma an sami gibi sai a cika masa, amma gaskiya cikon ne dai ya fi biyo baya.
Haka kuma ya ce bayan sun si yi kayan abincin “sai su ajiye shi, idan yai tsada sai a futo da shi, abun da yasa na ja baya da harkar shi ne yadda hakan ke jefa al’umma cikin halin masti”, inji shi.
Shi ma wani wanda ya watsar da wakilcin masu sayen kayan amfanin gonar tun suna yabanya, ya ce abu ne wanda in kana yi indai kana da imani dole hankalinka ya tashi, domin suna saka kudi masu yawa, wasu Naira miliyan ɗari, wasu miliyan ɗari huɗu ko miliyan ɗari biyar suna iya bayarwa duk yadda ta kama, kawai su buƙatarsu ka tara musu kaya.
Ko me ke sa manoman sayar da kayan amfanin gonar na su a tsaye?
Nasir Garba wani manomi ne a jihar adamawa, ya ce saboda yadda suke da bukatar kudi, don sauke dawainiyar noman yasa suke siyar da kayan amfanin tun gabanin sun girbe su.
“Kaga ana buƙatar ƙudi, ga taki muna siyan sa naira dubu Arba’in ko sama da hakan, ga maganin feshi, ga biyan masu aiki, ga man fetur shi ma da muke siyan lita sama da naira dubu ɗaya, shi yasa muke kira ga gwamnati da ta bamu tallafin kayan noma”, in ji Nasir Garba.
Ƙungiyar dai da ta gano illar irin wannan ciniki na falle dai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da ‘yan majalisar dokoki, da su haramta sayen kayan amfanin gona ana kimshewa, sai sun yi tsada a fito da su, a sayar da dan karen tsada, kuma a inganta hanyoyin tallafa wa manoma.
”Idan aka yi girbi, aka kuma sami amfani mai yawa, sai a cika musu kudinsu, sannan su kwashe amfanin a motoci, su ɓoye , ba za a futo da su ba sai an ji farashin abincin ya tashi, wasu ma ƙayyade adadin farashin suke na cewar sai ya kai wani mataki sannan zasu futo da shi su siyar” in ji Kwamred Abubakar AbdusSalam.
Source: BBC Hausa