Manufar Mu
______________
Manufar HausaFarmers ita ce yaɗa ilimin noma da kiwo a zamanance cikin harshen Hausa a sauƙaƙe ta hanyar rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da kuma sautuka domin Hausawa da dukkanin masu sha’awar harshen Hausa. Kafar ta mayar da hankali kan wayawarwa da alummar hausawa kai wajen harkpkin noma da kiwo ta shafukan sada zumunta, yanar gizo da kuma su seminer da workshop. Bayan haka, shafin ya ba da damar aika tambaya kai tsaye. Ma’aikatanmu za su nazarci waɗannan tambayoyi tare da ba da amsoshinsu cikin lokaci.
Za a iya taimakawa da ilimin da ake da shi ko wanne iri ne ta hanyar danna wannan koren rubutun ko shafinmu na Wallafa Rubutu.
Ba manufarta ba ne tallata wata haja ta wata aƙidar siyasa ko rayuwa. Sannan, ba huruminta ba ne tallace-tallacen rayuwa da kuma kayan kasuwanci ko bakuma labaran yau da kullum ba.
HausaFarmers ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa.