Noman tumatir🍅 na latti inji Hausawa😂, Off-season inji turawa
Amatsayinku na manoma bawai kadai iya shukawa da kula da shukokinmu shine Abinda yafi kamata mu iyaba, Sanin lokutan da idan kashuka abu zaizo bashi sosai a kasuwanni yanada matuqar muhimmanci, sabida wannan ilimin ka iya janyo maka riba ×100% doriya akan ribar daka saaba samu a harkarka ta gona.
Misali: Idan muka dauki tumatir🍅 misali; a yanzu haka kwandon tumatir bai wuce #20,000 a kasuwanni sabida kusan a al’ada yawancin manomansa suna faara girbi daga watan (February-March) qarshe inda daga nan tumatir🍅 zai faara qaranci har zuwa (July) lokacin da na damina zai faara zuwa. To kaga wannan lokacin daga (May-June) lokacine Wanda Duk Wanda yakeda tumatir Zaka iya nemansa ka rasa a kasuwa, sekaji ana tumatir seme kudi, inda musamman (June) zakaji Farashin kwandon nakai (#100,000-#150,000), irin wannan tumatir shi ake kira (Off-season).
To menene qalu-bale game da Off-season?
Shi wannan kalan tumatir na latti yana buqatar manomi yakasance ya koyi wasu dabarun noma da ilimin zamani na kimiyyar noma yazo dasu.
1. Kasancewar ana faara rainon irinsa daga tsakiyar watan biu zuwa farkon watan uku (15th/feb-5th/march) a dasashi tsakiya zuwa qarshen march din, idan muka lura wannan lokacine na zafi sosai a al’adar Arewacin Nigerian, kuna lokacine wadda cututtukan tsirrai suke qaruwa musamman (Fungal da bacterial diseases) wadanda baa cika samunsu lokutan sanyiba kuma suna matuqar illata tumatir idan manomi baisan matakansuba. Dole manomi yadinga amfani da (Fungicide irinsu Mancozeb, maneb, azazystrobin, Copper-oxide da makamantarsu don tseratar da tumatir dinsa daga wannan cuta tundaga Lokacin raino har zuwa girbi.
2. Kasancewar Akwai zafi sosai kuma zafin qasa dake tasowa yana taimakawa wajen kawo wadannan cututtukan, ana zuba ciyawa ko karmami ko ayi amfani da leda rufe kuyya(plastic mulch) a rufe kuyyar kafin yin dashe kanta. Sannan kuma kada ayi wasa da ruwa akai akai fiye da lokacin sanyi, sannan kuma a daureshi tumatir din da igiya (Staking) hikinam hakan shine kada tumatir din ya kwanta a qasa ko yayan sabida kada su dauki cuta.
3. Me muhimmanci sosai shine; Neman iri (trophical seed) Wanda musamman masana sunyishi don irin wannan lokaci me juriya sosai kamar irin (PLATINUM F1) na kamfanin EAST-WEST SEED. Ba kowani irine ke iyayi yadda yakamataba, amma kada kaga tsada Akwai biyan buqata.
4. Sannan a lokacin da manomi kake gyaran kuyyoyinka ka tabbatar ka zuba musu takin gargajiya(Manure) , Manomi zaka iya hada (Toka, kashi shanu ko kaji dakuma dussan shinkafa) ka juyasu seka ruba, sannan takin zamani kadan-kadan amma akai-akai. Wadannan sune daga shawarwari don kaucewa wadancan qalu balai.
SHAWARA
Manomi kada kace sekabude katon fili donyin tumatir a irin wannan lokacin aa. Kayi planning gwargwadon qarfinka, ida fuloti daya zaka iya koma rabi(1plot or half) kayishi ka gyara shi sosai, shi wannan ko yaya kayishi yanazuwa da daraja sosai. Idan kuma kanada hali sosai(kudi) to sekayi ‘Greenhouse’. Zamu sami lokaci zamuyi bayani kan Greenhouse, Screenhouse da sauransu InshaAllahu. Kada macene dake zaune a gida kuma gidan Akwai ruwa kuma Akwai space, to ina bada SHAWARA tashiga wannan harkar don Akwai Alkhairy sosai.
Gamasu neman iri, kowani abu daya Shafi noma ko wani kala, ko neman shawara, kokuma so kake aje gonarka/ki amuku tsari da shawarar(Consultation) zaku iya nemanmu ta 07068489695.D.mbk
Mun karu kwarai da wannan dimbin ilimi. Allah Ya bada lada.