TAKI(Fertilizer)
MENENE TAKI?
Taki shine duka wani sinadari (nutrient) wanda shuka (plants) ke buqata don samarda amfani me yawa da inganci.
MUNADA TAKI KASHI BIYU 2.
….Takin Gargajiyan(Organic Manure)
….Takin Zamani(Inorganic Fertilizer)
1. Takin gargajiya (organic manure): Shine takin da asalinsa daga abu me rai ya fito. Misali Kashin shanu, kashin kaji, raunon shinkafa, raunon masara, tushen waken soya da makamantarsa, rubabben ragin kifi, rududdugaggun tuwasun kayan lambu wadanda aka cire, ‘Green manure’, dama sauransu dayawa.
MENE AMFANIN TAKIN GARGAJIYA GA SHUKA (manure)?
1- Yana dauke da wasu sinadarai masu muhimmanci wadanda shuka keso kuma basu a takin zamani (micro nutrients) kamar Molybdenum, Boron, chlorine, Iron, Nickel, zinc, copper dama sauransu.
2- yana qarawa qasar gona riqe ruwa na tsawon lokaci (water holding capacity).
3- yana ajiye masurai a qasa wadanda keda alaqa ta mutaimaki juna da amfanin gona (Mutualism).
YAYA AKE ZUBA TAKIN GARGAJIYA A GONA)?
– KASHIN SHANU: Ana zuba 2kg a duk 2m² (qafa biu)
– KASHIN KAJI DA SAURAMSU: zaka iya zuba qasa da haka sabida adadin sinadarin ‘NITROGEN ‘ dake cikinsu yafi na kashin shanu yawa ( Buhun Kashin kaji ashirin 20 daidai yake da buhun Takin zamani na UREA daya ta adadin NITROGEN dake cikinsu, kashi 46% na takin UREA nitrogen ne.)
Ana zuba takin zamani ta hanyar watsashi kokuma zubashi tushe-tushe ko a gurbin shuka sati biu kafin shuka idan bai Riga ya rubeba.
GARGAD: ayi la’akari da adadin da muka ambata a sama sabida kada a zuba ya kasa kokuma a cika.
– GREEN MANURE: Ga wadanda basuda kashin kaji kona shanu ballantana Compost dayayi tsada, ana GREEN MANURE ta hanyar shuka waken soya a gona kusa-kusa kafin ayi huda, sekabar waken soyan yafito yakai gab dazaifara fure, seka hude gonar ka binne shi. Wanna shine green manure. Shima dai – dai yake da ko yamafi zuba takin gargajiya. Bari mu taqaita a nan. Za,aji bayanin takin zamani a rubutunmu na biyu (Part 2)
Bissalam.