Noman Kifi da Ribar Sa
Noman kifi na da kaso sama da 50% na kasuwar kayan kifi a duniya. Dubban ‘yan Afrika na shiga wannan sana’a kowacce shekara. Noman kifi yana daya daga cikin hanyoyin kirkirar aikin kai a Najeriya, amma tabbas yana daya daga cikin bangarorin aikin gona da aka yi watsi da su a Najeriya.
Gaskiya ne cewa akwai dama mai yawa na samun kudi a bangaren aikin gona da yan Najeriya suka yi watsi da su. Wannan ba wai kawai yana bunkasa kasar ba ne, har ma yana taimakawa wajen kawar da rashin aikin yi da bunkasa tattalin arziki.
Noman kifi yana da riba kuma ana yin sa sosai a fadin Najeriya da sauran kasashen duniya da dama.
– Kayayyakin Kifi: Kayayyakin kifi na daya daga cikin abubuwan da ake nema sosai kuma ake ci a Najeriya, saboda yana da arha fiye da nama, wanda hakan ya sa ya zama abinci mai rahusa.
– *Farashin Farawa da Gudanar da Gonar Kifi*: Farashin farawa da gudanar da gonar kifi yana da arha idan aka kwatanta da sauran dabarun kasuwancin noma da yawa. Haka ramin kifi da sauran matakan da suka dace kana iya yin su da kanka ko da abokanka, babu buƙatar biyan kuɗi aikin leburanci.
– Kasafin Gudanarwa Mai Rahusa: Yana da kasafin gudanarwa mai rahusa saboda ciyarwa sa da kuɗin gudanarwa mai rahusa ne. Gina ramin kifi yana buƙatar fili a bayan gidanka, misali, fili mai tsawon mita 7 da faɗin mita 10.
– Kuma, Noman Kifi yana samar da hanyoyin samun kuɗi da aikin yi. Haka kuma, noman kifi yana taimakawa wajen ceton wasu nau’in kifaye irin su cod, sea bass, da red snapper, ta hanyar farfaɗo da yawan su ta hanyar noman kifi (aquaculture).
### Sauran Bukatun Noman Kifi:
– Samar da Ruwa (za ka iya ɗebo daga wani kogi kusa da kai).
– * Kiwon Rami* (Kiwon rami yana taimakawa wajen daidaita zafin ramin kuma yana sa ramin yayi kama da yanayin su na dabi’a kogi ko teku). Idan ba ka san yadda za ka gano wannan kasar kiwon rami ba, za ka iya ɗauka daga wani ramin kifi na kusa da kai.
– Cement (don gina ramin kifi).
Duk da cewa wasu kasuwancin noma na iya samun asara idan ba a kula da su yadda ya kamata ba, kayan noman kifi suna da ƙarancin haɗarin asara.
### Yin Ramin Kifi:
Za ka iya tono rami mai tsawon mita 7 da faɗin mita 10 a fili da aka ware, mai zurfin kafa 2 zuwa 5, sannan ka rufe shi da cakuda siminti, yashi, da kuma qasa me taushi (ana yin wannan ne don hana ruwa yin yawo zuwa ƙasar da ke zagayen).
Sannan ka cika shi da ruwa (yana da matukar muhimmanci a cika ramin da ruwa sannan a zubar da shi sau biyu zuwa hudu domin cire sinadarai masu haɗuwa da siminti). Ka shuka ciyawa; ka bari ramin ya zauna tsawon sati ɗaya ko fiye kafin ka shigar da ƙananan kifaye (fingerlings).
NB: Za a iya kawata saman da kewaye da ramin kifi yadda ka ga dama.
Banda ribar da ake samu daga noman kifi, kayan kifi na ba da sinadarin furotin wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyarmu.
### Nau’in Noman Kifi
Akwai nau’ikan noman kifi daban-daban gwargwadon wanda kake son shiga;
Noman Kifin Catfish
Wannan shi ne mafi shaharar kasuwancin noman kifi a Najeriya, saboda shaharar nau’in kifin. Haka kuma, kifin catfish shine mafi yawan kifin da ake amfani da su a cikin abincin Afirka a gidaje da dama, gidajen cin abinci, taruka, otel-otel da sauransu. Bukatar su da saukin kiwo su ya sa mafi yawan manoman kifi ke mai da hankali kan noman kifin catfish maimakon wasu nau’ikan kifaye.
Noman Kifin Tilapia
Wannan su ne kifi na biyu mafi shahara da ake amfani da su a cikin abincin Najeriya. Suna da muhimmanci a noman kifi a fadin duniya saboda yadda kifin ke girma da sauri, yana da juriyar rayuwa acikin kifaye masu yawa da kuma yanayin ruwa mara inganci, waɗannan abubuwan sun sa su zama nau’in kifi mai amfani ga manoman kifi.
Noman Kifin Salmon (Mackerel)
Kifin Salmon na da kaso mai yawa na kayan kifi da ake ci a Najeriya. Sun fi shahara da sunan “Titus” a Najeriya kuma gidaje miliyoyi ke saya a kullum.
Haka kuma, ana noman su a gonakin kifi.